Za a fara yakin neman zabe na 'yan majalisu a Guinea

Shugaba Alpha Conde na Guinea
Image caption Kasar Guinea na fuskantar zabe

Shugaban Kasar Guinea Alpha Conde ya shammaci 'yan kasar, ya sanar da wata doka kwatsam wadda ke shelar fara yakin neman zabe na majalisar dokoki a wata mai zuwa.

Shugaba Conde yace za a yi yakin neman zaben har zuwa ranar 28 ga watan na Yuni kwanaki biyu gabanin zaben.

An dai sha dage zaben saboda koke-koken da 'yan adawa ke yi na cewar gwamnati tana shirin yin magudi.

'Yan adawar sun yi barazanar kauracewa zaben.

Mutane a kalla goma sha-daya aka kashe a dauki ba-dadin da aka shafe kwanaki ana yi cikin makon jiya tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan 'yan adawa.

Karin bayani