An zargi 'yan sandan Kenya da cin zarafi

Image caption Wasu jami'an tsaron Kenya

Ƙungiyar Human Rights Watch ta wallafa wani rahoto game da zargin ganawa mutane azaba da fyaɗe da ake zargin 'yan sandan Kenya na aikatawa galibi akan 'yan gudun hijirar Somalia.

Yawancin lamarin dai ya auku ne tsakanin watan Nuwamba na shekara ta 2012 da kuma watan Janairu na 2013.

Rahoton yayi ikirarin an fara wannan cin zarafi ne jim kaɗan bayan wani harin gurneti da aka jefa a kan wata motar safa a watan Nuwamba a unguwar Eastliegh ta Kenya, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane bakwai.