Mahama ya yi gargadi kan rashin tsaro

Shugaba John Mahama
Image caption Yankin Yammacin Afirka na fuskantar barazana ta tsaro

Shugaban Kasar Ghana John Mahama ya yi gargadin cewa, gwagwarmayar kungiyoyi masu kishin Islama na barazana ga zaman lafiya a yammacin Afrika.

Kodayake gwagwarmayar ta 'yan kishin Islama ba ta shafi Kasar Ghana ba kai-tsaye, Mr. Mahama ya ce babu wata Kasar da lamarin ba zai shafa ba idan har aka kyale masu tayar da kayar bayan suka kafu a wasu wurare.

Yace, tsoma bakin da Kasar Faransa ta yi cikin hanzari ya taimaka wajen daidaita lamura a Kasar Mali, to amma yace har yanzu tsugune ba ta kare ba a can.

Mr. Mahama ya yi kiran da a kafa wata rundunar maida martani ta musamman ta Afrika da za ta zamo cikin shirin ko-ta-kwana.

Karin bayani