Kotu ta hana karin albashin 'yanmajalisa a Kenya

Masu zanga zanga a Kenya
Image caption Masu zanga zanga kan karin albashin yanmajalisa a Kenya

A Kenya wata kotu ta hana yan majalisar dokokin kasar daga yin kari kan albashinsu.

Hakan ya biyo bayan wata karar da kungiyar lauyoyi ta Kenyar ta shigar ne tana neman da a dakatar da yan majalisar daga baiwa kansu albashi mai tsoka dukkuwa da cewar hukumar shata albashi da sauran hakkokin ma'aikata ta rage albashin nasu da rabi.

Alkalin babbar kotun ta birnin Nairobi, David Majanja ya umarci hukumar kula da ma'aikatan majalisar dokokin Kenya kada ta aiwatar da maida albashin 'yan majalisar dokokin zuwa dalar Amurka dubu goma da 'yan majalisar suka zartar makon nan.

Cikin wannan makon ne dai 'yan majalisar dokokin Kenya suka amince da wani kuduri da yayi watsi da matakin da hukumar kayyade albashi da kuma alawus ta gwamnatin Kenya ta dauka na rage albashin 'yan majalisar da rabi.

Hukumar dai tace, ta dauki matakin rage albashin 'yan majalisar ne saboda matsin tattalin arziki ba zai bari a cigaba da aiwatar da albashin ba.

Matakin da 'yan majalisar dokokin Kenya suka dauka na yin watsi da ragin da aka yiwa albashinsu ya fusata 'yan kasar ta Kenya da dama da suka hada shugaban kasar, Uhur Kenyatta.

Tun ma kafin a kai ga wannan dai masu zanga-zanga da suka fusata sun gudanar da zanga-zanga a harabar majalisar dokokin inda suka saki aladu domin nuna alamar handama.