Najeriya: Rashin waya ya yanke harka

Image caption Rashin layukan waya a jihohin da aka ayyana dokar ta-baci ya jefa mutane cikin damuwa

Zainabu Yusuf, wacce ke zaune a yankin arewa maso gabashin Najeriya ita da 'ya'yanta biyu, ta cika da takaici.

A tsawon kwana uku ta kasa magana da danta Ahmad, wani dan tireda a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Da ma dai layukan waya daga Yola, inda take zaune, zuwa Maiduguri, ba su cika kyau ba tun bayan da mayakan Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad—kungiyar da aka fi sani da suna Boko Haram—suka fara kaddamar da hare-hare a kan kayayyakin kamfanonin sadarwa a yankin.

Ga shi yanzu abubuwa sun kara lalacewa matuka sakamakon ayyukan da sojoji ke gudanarwa a yankin bayan da aka ayyana dokar ta-baci a jihohin biyu da ma Jihar Yobe mai makwabtaka da su kusan makwanni biyu da suka gabata.

Jami'an tsaron na fafutukar ganin sun raba jihohin da tayar da kayar bayan da ya jefa kasar cikin rikici mafi muni da ta fada tun bayan yakin basasar shekarun 1960.

Image caption Taswirar Najeriya mai nuna yankunan da dokar ta-bacin ta shafa

A cewar kafofin yada labarai na kasar, a wani bangare na aikin da sojojin ke yi, an zargi hukumomi da katse hanyoyin sadarwa ta wayar salula a yankin a yunkurinsu na hana masu tayar da kayar bayan amfani da hanyoyin.

An dai bayar da rahotannin cewa masu tayar da kayar bayan kan yi amfani da wayoyin na salula don tashin bama-bamai da kuma sadarwa a tsakaninsu.

Sai dai kuma hukumomin ba su tabbatar da cewa su suka katse layukan sadarwar ba.

A daidai wannan lokacin ne kuma Malama Zainab ta yi yunkurin kiran danta ta waya ba ta yi nasara ba.

A cewarta, cikin sanyin jiki, "Kwana uku ina ta kokari amma ban same shi ba, kuma ban iya samun kowa daga cikin abokansa da ke can ba, balle su hada ni da shi mu yi magana".

Ta ki ta yi karin bayani dangane da halin da take ciki; sannan ta ki ta bari a dauki hotonta.

Ta kara da cewa: "A rana ta hudu wayata ta yi kara sai na ga bakuwar lamba—ba lambar Najeriya ba ce—amma da na daga sai na ji muryarsa".

Shi Ahmad din ya yi kokari ya yi magana da mahaifiyarsa amma abin ya ci tura, kuma ranar da ya same ta ba a ainihin cikin birnin Maiduguri yake ba; yana Gamboru Ngala ne, wani gari dake kan iyaka, kusan kilomita 140 daga Maidugurin.

"A can ne", inji Malama Zainab, "ya samu layin wayar Kamaru, ya kuma kira ni".

Layukan wayar salula na Najeriya ba su da kyau a yankin, don haka mazauna suka koma amfani da layukan waya na Kamaru don samun damar yin magana da 'yan uwansu 'yan Najeriya, kamar yadda wani mazaunin yankin, Sani Gamboru, ya shaida wa wakilin BBC ta layin wayarsa na Kamaru.

Hatta a Jihar Adamawa, inda babu masu tayar da kayar bayan sosai, kuma babu ayyukan soji sosai, layukan wayar salula ba su da kyau.

Hasali ma, da safiyar ranar Litinin samsam layukan waya ba sa samuwa a Yola.

Abdurrazak Namdas, wani dan siyasa kuma mawallafin jarida da ke goyon bayan ayyana dokar ta-bacin "saboda watakila ita ce hanya mafi inganci ta kawo karshen tayar da kayar baya", ya bayyana takaicinsa da matsalar rashin wayar.

"Na kasa samun mutanena kamar yadda na saba", in ji shi. "Sai ka yi ta buga lamba kafin ka samu ta shiga; sannan wani lokaci idan ka samu ta shiga, kafin ka gama magana ta katse. Abin da ban takaici matuka".

Sai dai duk da matsalar sadarwa da ake fuskanta, Malama Zainab ta yi farin ciki saboda musayar wutar da sojoji ke yi da masu tayar da kayar baya ba ta shafi danta ba. Amma fa ta damu matuka saboda ya ki ya ji shawararta ya koma gida.

Ba wannan ba ce kadai damuwarta. Tana kuma fama da rashin ciniki a gidan sayar da abincinta dake Yola saboda dokar hana fita daga almuru zuwa wayewar gari.

Image caption Wuraren kasuwanci na kukan rashin ciniki

Kuma ba ita kadai ke fuskantar wannan matsala ba. Nnamdi Nwedu, mai shagon sayar da barasa na Happy Day Bar, daya daga cikin shahararrun wuraren shakatawar dare a Yola, shi ma yana fuskantar rashin ciniki.

A cewarsa, cinikin da ya kan yi ya ragu da kashi saba'in zuwa tamanin cikin dari.

Ko da yake Mista Nwedu ya ki bayyana hakikanin abin da ya kan samu kafin ayyana dokar ta-bacin, daya daga cikin ma'aikatansa ya ce su kan yi cinikin da ya haura naira 250,000 (kwatankwacin dala 1,600 ko fam 1,000) a kullum.

Kafin kafa dokar hana fitar dai, Happy Day Bar kan bude da da yamma ne a kuma rufe bayan karfe goma sha biyun dare, ko ma da asuba wani lokaci a karshen mako.

Dokar da aka kafa yanzu ta hana fita daga karfe bakwai na yamma zuwa karfe shida na safe ta hana hakan.

A cewar Mista Nwedu, "Mu ba adawa muke yi da matakin gwamnati ba saboda mai yiwuwa akwai abin da suka gani kafin su ayyana dokar ta-baci su kuma kafa dokar hana fita.

"Amma kamata ya yi su fahimci cewa wannan al'amari yana shafar mutane—kananan 'yan kasuwa".

Yayin da yake wannan bayanin, daya daga kwastomominsa, Othman Joseph, wanda ke zaune a wani teburi da kwalbar barasa a gabansa, ya ce: "Ga shi kana gani na ina shan barasa da rana saboda dokar hana fitar dare. A da na kan kai har karfe dayan dare a nan, amma yanzu dole na koma gida karfe biyar na yamma".

A kusa da shagon barasar kuma akwai wani mai balangu, Sani Muhammad, wanda shi ma yake kukan rashin ciniki.

"Kafin kafa dokar", in ji shi, "mukan yanka, mu kuma gasa raguna biyar a kullum. Amma yanzu daya kawai muke yankawa kuma da kyar muke sayar da shi".

Su ma malaman addinin Musulunci dokar tana bata musu rai saboda tana hana Musulmi yin sallar asuba da ta isha'i a masallaci tare da jama'a—al'amarin da ya sa Majalisar Musulmin Adamawa ta yi kira da a sassauta dokar.

Amma yayin da wadannan mutane ke fushi da dokar ta hana fitar dare, an ce matan aure da dama suna farin ciki da ita.

Daya daga cikinsu, wata malamar makaranta wacce ba ta so a ambaci sunanta ba saboda ba ta so ta bata ran maigidanta, ta shaidawa wakilin BBC cewa kafa dokar ya kara dankon kauna a tsakanin iyalanta.

A cewarta, "Mu dokar ta yi mana kyau. Yanzu muna samun lokaci mu zauna mu yi hira. Ranar farko da maigidana ya dawo gida da karfe shida na yamma 'yarmu mai shekaru hudu da haihuwa murna ta yi ta yi".

Sai dai fa akwai iyalan da ba sa murna saboda hauhawar farashin kayayyaki sakamakon tattare hanyoyi da kuma rufe iyakokin kasar da wadansu kasashe a jihohin da al'amarin ya shafa.

Wuraren binciken ababen hawa na sojoji da 'yan sanda da aka kakkafa a cikin jihohin da ma kan iyakokinsu da sauran jihohi suna takaita zirga-zirgar ababen hawa.

Haka zalika, hukumomin Najeriya sun rufe iyakokin kasar da Nijar, da Kamaru, da Chadi masu makwabtaka, al'amarin da ya dakile shige da ficen mutane da kayayyaki zuwa ko daga wadannan wurare.

Alal misali, a Maiduguri, rahotanni sun nuna cewa farashin muhimman kayan masarufi, kamar shinkafa da omo, ya tashi da kusan kashi talatin cikin dari.

Wani mazaunin birnin ya bayyana cewa: "Mudun shinkafar da a da muke saya naira 500 (kwatankwacin dala uku, ko fam biyu) yanzu naira 630 ne".

Image caption Wannan ne aiki mafi girma da sojojin Najeriya ke yi tun bayan yakin basasar shekarun 1960

Mazauna birnin Yola sun ce ba su fuskanci irin wannan hauhawar farashi ba amma kuncin da dokar hana fitar ta haifar da kuma karar harbin bidiga da sukan ji cikin dare na daga musu hankali.

Hukumomi dai sun ce karar harbin da mutane ke korafi a kai harbin iska ne da jami'an tsaro masu sintiri ke yi don tsorata masu yunkurin yi wa dokar karan-tsaye.

A cewarsu akasarin sojojin da aka tura Jihar Adamawa an kai su wadansu wurare ne, inda aka yi amanna mutanen da ake zargi masu tayar da kayar baya sun buya.

Mazauna birnin Yola da dama dai na fatan dokar ta-bacin za ta zo karshe nan ba da jimawa ba.

A cewar wani ma'aikacin kamfanin sadarwa, "Ba ma iya magana da abokanmu da iyalanmu ta waya, sannan harkokinmu na kasuwanci ba sa tafiya. Dubi yadda na zauna ba abin da nake yi saboda dukkan layukan sadarwa ba sa aiki".

Karin bayani