Zaman dar-dar ya karu a Gabas ta Tsakiya

Shugaba Bashar Al-Assad
Image caption Shugaba Bashar Al-Assad

Zaman dar dar na ci gaba da karuwa a yankin gabas ta tsakiya sakamakon rahoton da ke cewa, Shugaba Bashar Al-Assad na Syria ya ce tuni ya karbi kashin farko na makaman kakkabo jiragen sama daga Rasha, samfarin S-300.

Tuni dai Isra'ila ta yi gargadin cewar za ta mayar da martani akan wannan mataki.

Sanarwar ta fito ne a cikin wata hira da za a watsa nan gaba a yau, a gidan Talabijin din kungiyar 'yan Shi'a ta Hezbollah da ke Lebanon.

A yanzu haka dai mayakan Hezbollah sun shiga dumu dumu cikin fadan da ake ci gaba da tafkawa don samun iko da muhimmin garin Al-Quseir na yammacin Syria.

Karin bayani