Yau ne ranar yaki da shan taba sigari

Image caption Taba sigari nada illa ga dan adam

Majalisar dinkin duniya ta kebe kowacce ranar 31 ga watan Mayu, a matsayin ranar yaki da shan taba sigari a fadin duniya.

Taken wannan shekara shine "haramta tallace-tallacen taba sigari da kuma yadda kamfanonin tabar ke daukar dawainiyar wasu aikace aikace ko wasanni".

A kowace shekara dai a irin wannan rana a kan dauki matakai na wayar da kan jama'a wajen illolin da ke tattare da shan taba sigari da kuma duba hanyoyin da za a bi domin shawo kan matsalar da ke sanadiyyar mutuwar mutane masu yawa.

Hukumar lafiya ta duniya-WHO ta ce mutane kusan miliyan shida ne kan rasa rayukansu sakamakon shan taba-sigari a duk shekara.

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa shan taba sigari na haddasa cututtuka da dama, da suka hada da sankarar huhu, da kuma sanyin huhu wato Pneumonia.

Karin bayani