Majalisar Najeriya ta amince da hana auren jinsi

Image caption Majalisa a Najeriya ta yi dokar haramta auren jinsi

Majalisar wakilan Najeriya ta amince da wata doka wadda ta mayar da aure tsakanin 'yan luwadi da madugo babban laifi, tana mai cewa za a iya zartarwa wanda ya keta dokar hukuncin daurin shekaru goma sha hudu a gidan yari.

Dokar ta haramta rijistar kungiyoyi na 'yan luwadi da madugo da nuna soyayya tsakanin masu jinsi daya a bainar jama'a.

Majalisar dattawan kasar ce ta fara amincewa da dokar watanni goma sha takwas da suka wuce,.

Sai Shugaba kasar, Goodluck Jonathan, ya rattaba hannu a kan ta ne za ta zamo doka.

Masu sukar lamirin dokar sun yi gargadin cewa za ta iya shafar tallafin da kasashen waje ke bai wa Najeriya a bangaren yaki da cutar kanjamau, ko wasu cututtuka masu alaka da ita.

Sai dai majalisar wakilan ta yi marhabin da duk matakin da kasashen waje za su dauka sanadiyar zartar da wannan doka.

Karin bayani