Mayaƙan 'yan tawaye sun doshi Qusair

syria
Image caption 'Yan tawayen Syria

Mayaka masu yawa sun isa birnin Qusair don taimakawa 'yan tawaye a gumurzun da suke yi tsakaninsu da gwamnatin Syria wacce Hezbollah ke tallafawa.

Wata majiya a Qusair, ta shaidawa BBC cewar adadin mayakan bai kai dubu daya ba, kamar yadda shugaban riko na babbar kawance 'yan adawa, George Sabra ya bukata.

Zuwansu bai saba da rahotannin kafar yaada labaran gwamnati a kan cewar an yiwa garin ?awanya.

Shugaban Bashar al-Assad tunda farko ya shaidawa gidan talabijin na Lebanon cewar ya yi "ammanar zai samu nasara" a tashin hankalin da aka shafe shekaru biyu ana fafatawa.

Dakarun gwamnati, masu samun goyon bayan ?ungiyar 'yan shi'a ta Hezbollah, na ?ara nausawa zuwa Qusair, inda suke da iko da kowacce mashiga.

Gidan talabijin na Syria ya ce dakarun gwamnati da mayakan Hezbollah sun kwace lardin Arjun dake Qusair din a ranar Alhamis.

Karin bayani