Assad na Syria ya gargadi Isra'ila

Image caption Shugaba Assad na Syria ya gargadi ISra'ila

Shugaban kasar Syria Bashar al Assad ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kwantaragin siyan makamai da Kasar Rasha, ya kuma gargadi Israila kan harin sama.

Kasar Israila dai na kallon wannan a matsayin barazana ga tsaron kasarta kuma za ta iya mayar da martani.

Wannan na zuwa ne lokacin da wani likita a birnin Qusair na Syria ke cewa mutane fiye da dari shida da suka ji rauni sun makale a yankunan da 'yan tawayen suka mamaye, babu damar samun taimakon magani.

Wannan batun makaman dai ya ja hankali sosai.

Shugaban ya kuma gargadi Isra'ila cewa matsawar ta sake kai mata hari ta sama, to fa wannan karon Sojin Syrian za su mayar da martani ayi gaba da gaba.

Yakin dai da aka shafe sama da shekaru biyu ana yi ya jefa 'yan kasar cikin mawuyacin hali.

Karin bayani