Iraki ta zargi Al-qaeda da shirin kai harin makamai masu guba

Makamai masu guba
Image caption Makamai masu guba

Hukumomin Iraqi sun ce, sun gano wani shirin kungiyar Al Qaeda na yin amfani da makamai masu guba a cikin kasar, da kuma shirin shigar da makaman masu guba kasashen Turai da kuma Amurka.

Kakakin ma'aikatar tsaron Iraqin, Muhammad Al Askari yace, masu binciken tattara bayanan tsaro na soja, sun gano wasu wurare uku inda ake hada makamai masu guba.

Muhammad Askari ya kuma fadawa gidan talabijin na Iraqin cewa, an kama mutane biyar dangane da wannan lamari, kuma dukkansu sun amsa laifin da ake zarginsu da shi.