Japan zata zuba jari sosai a Afirka

Image caption Praministan Japan da kuma shugaban Habasha

Japan tayi alƙawarin bada tallafi da kuma zuba jari na kimanin dalar Amurka biliyan biyu a ƙasashen Afurka, yayin da take ƙoƙarin kamo ƙafar China, wacce yanzu haka take kan gaba wajen zuba jari a nahiyar Afurka.

Yawancin tallafin da za'a bayar cikin shekaru biyar zai maida hankali ne ga samar da ababan more rayuwa da kuma inganta hanyoyin sufuri musamman a manyan biranen nahiyar Afurka.

Praministan Japan Shinzo Abe ya fadawa taron bunkasa kasashen Afurka da ake yi a birnin Yokohama cewa, Japan zata maida hankali ne ga zuba jari a fannonin kasauwanci da dama.

Shinzo Abe abinda ƙasashen Afurka ke buƙata yanzu shi ne zuba jari daga 'yan kasuwa masu zaman kansu, domin samun damar haɗa gwiwa tsakanin 'yan kasuwa da gwamnati wajen yin ayukan da zasu tallafa wajen bunƙasa rayuwar al'umma.