Nijar: An kai hari a gidan kaso na Yamai

Wurin da aka kai harin ƙunar baƙin wake a Agadez kwanki goma da suka gabata
Bayanan hoto,

Wurin da aka kai harin ƙunar baƙin wake a Agadez kwanki goma da suka gabata

Yau ne gungun wasu 'yan bindiga suka kashe jami'an tsaro a ƙalla biyu yayin da suka kai hari a babban gidan yarin Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijar.

Kafofin yaɗa labari sun ambato kakakin gwamnatin Nijar ɗin kuma ministan shari'a, Marou Amadou yana tabbatar da aukuwar lamarin.

Wannan hari dai na zuwa ne kusan kwanaki goma bayan tagwayen harin ƙunar bakin wake da aka kai a Nijar din, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane ashirin.

Wani da ya shaida lamarin yace, kusan tsakar rana a yau ne mazauna kusa da inda lamarin ya auku suka soma jin karar harbe-harbe, lamarin da ya firgita jama'a.

Was kungiyoyin gwagwarmaya na masu kaifin kishin Islama da suka hada da MUJAO ne suka yi ikirarin cewa, su suka kai harin na ranar 23 a watan Mayu da ya gabata.

Kuma sun ce, sun kai harin ne saboda maida martani ga kai ɗaukin soja da Nijar ta kai a arewacin Mali.