Erdogan ya bukaci a kawo karshen zanga zanga a Turkiya

Masu zanga zanga a Turkiyya
Image caption Masu zanga zanga a Turkiyya

Ana ci gaba da zanga zanga a wasu sassa a kasar Turkiyya duk kuwa da janyewa da 'yan sanda su ka yi a dandalin da aka fara zanga zangar.

Prime Minsitan kasar Recep Tayyip Erdogan ya ce yan sanda sun yi kuskuren amfani da karfi amma yayi kira da a kawo karshen zanga zangar Istanbul din.

Ministan harkokin cikin gida na Turkiyya Muammer Guler ya ce an kame kimanin mutane dubu daya a zanga-zangar nuna kiyayya ga gwamnati dake gudana a Istanbul da sauran wasu birane.

An ci gaba da arangama tsakanin jami'an tsaro da dubban masu zanga-zangar a rana ta biyu, yayinda 'yan sanda ke amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi don fatattakar su.

Wani wakilin BBC a Istanbul ya ce masu zanga-zangar sun nuna farin cikinsu yayinda suke rawa suna tafa hannuwa a dandalin na Taksim.