Zanga-zanga na karuwa a Turkiyya

Image caption Zanga-zangar Turkiyya na kara ruruwa

A kasar Turkiyya an shafe daren jiya ana cigaba da zanga-zanga bayan 'yan sanda sun yi arangama da dubban masu zanga-zangar a tsakiyar birnin Istambul.

An raunata mutane fiye da dari daya a yayinda jami'an tsaro suka yi kokarin tura masu zanga-zangar baya da barkono mai sa hawaye da ruwan-zafi a kusa da dandalin taro na Taksim.

An fara zanga-zangar ne a safiyar Jumma'a lokacinda 'yan sanda suka tarwatsa wasu masu zanga-zangar zaman durshan don nuna rashin amincewa da wani shiri na mayar da wani wurin shakatawa zuwa cibiyar ciniki.

Daga bisani zanga-zangar ta yadu zuwa wasu sassa na birnin Ankara da sauran birane, ta kuma kara fadada boren nuna rashin amincewa da gwamnati da jami'an tsaro wadanda ake zargin sun dauki tsauraran matakai a kan taron jama'ar.

Karin bayani