An tuhumi Michael Adobolajo da aikata kisan kai

Adebolajo da Adebowale
Image caption Adebolajo da Adebowale

'Yan sanda a nan Birtaniya sun tuhumi mutum na biyu da zargin kisan sojan Birtaniya a unguwar Woolwich kwanaki goma da suka gabata.

Wanda aka tuhuma din wato Micheal Adebolajo, ana zarginsa ne da kuma yunkurin kashe 'yan sanda biyu da kuma mallakar makami ba bisa ka'ida ba.

Mutum na farko da aka tuhuma da kisan sojan, Lee Rigby shi ne, Micheal Adebowale.

Kisan Lee Rigby ya janyo zamna fargaba ga al'ummar musulmi a Birtaniya bayan da wasu masu tsaurin ra'ayin kare Turawa sukarika zanga zanga suna kai hare-hare kan wasu musulmi ko masallatai.