Kano: Ƙwarori sun nisanta kansu daga makaman da aka kama

Image caption Tutar ƙasar Lebanon

Ƙungiyar 'yan ƙasar Lebanon mazauna Kano ta nisanta kanta daga zargin da jami'an tsaron Nigeria ke yiwa wasu ƙwarori na shigo da muggan makamai ƙasar.

A wani taron manema labarai da ƙungiyar ta ƙira ɗazu a Kano ta ce daga yanzu zata sa ido sosai akan ƙwarori dan kada a bata musu a bata musu suna.

A ranar Talatar da ta gaba ta ne dai hukumomin tsaron Nigeria suka gano wani gida na wani kwara a Kano makere da muggan makamai, waɗanda aka yi zargin ƙungiyar 'yan Shi'a ta Hezbullah ce ta shigo da su Najeriya.

Tahir Fadallah shi ne shugaban kungiyar ta warori mazauna Kano kuma yace, zai sa ido sosai akan dukkan ƙwarori mazauna Kano.