Za mu yi nasara a zaben 2015 —PDP

Nigeria pdo
Image caption PDP ta ce shugaba Goodluck Jonathan ya taka rawar gani

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta ce akwai kwararan alamu da ke nuna cewa za ta yi gagarumar nasara a zaben shekarar 2015 saboda kyawawan ayyukan da ta yi ikirarin aiwatar a shekaru biyu da suka gabata.

Kakakin Jam'iyyar, Olisa Metuh, ne ya bayyana haka a hirar da ya yi da Sashen Hausa na BBC.

Ya kuma soki jami'yyun adawar da ke yunkurin hadewa da zummar kalubalantar jam'iyyar, yana mai cewa nan gaba kadan za su tarwatse saboda ba su da wata manufa da ta wuce yunkurin kwace mulki daga hannun jam'iyyar.

Sai dai 'yan adawar sun ce jam'iyar ta PDP ba ta tsinanawa 'yan Najeriya komai ba, kuma da alama ta shiga rudu ne shi ya sa take irin wadannan kalamai.

A baya bayan nan ne shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya gabatar da rahoto kan ayyukan da gwamnatinsa ta yi a taron bikin komawar kasar kan tafarkin mulkin dimokaradiya.