Fursunoni 22 ne suka tsere daga gidan kaso a Yamai. In ji Marou Ahmadou

Taswirar Nijar
Image caption Taswirar Nijar

Gwamnatin Nijar ta ce yanzu dai an tabbatar da cewa, fursunoni ashirin da biyu ne suka tsere daga babban gidan yarin Yamai, babban birnin kasar jiya Asabar.

Ma'aikatar shari'a ta Nijar din ta ce, daga cikin wadanda suka tsere da gidan kason akwai 'yan ta'adda.

Ministan Shari'a, kuma kakakin gwamnatin ta Nijar, Malam Marou Ahmadou shi ne ya bada karin hasken a wata hira da manema labaru a Yamai.

Ministan ya kuma kara da cewa , wani karin soja daga cikin uku da aka raunata ya mutu, lamarin da ya kai sojojin da aka kashe zuwa uku.

Lamarin dai ya auku ne yayin da wasu dake tsare a gidan kason na Yamai suka yi kokarin tserewa, sai kuma wasu 'yan bindiga daga wajen gidan yarin suka harbe masu gadin kofar shiga gidan kason.

Gwamnatin ta ce babu makawa akwai hadin baki a wannan hari.

Karin bayani