Afrika ta Kudu za ta binciki kadarorin Gaddafi

Libya
Image caption Marigayi Muammar Gaddafi

Kakakin ministan kudi na kasar Afrika ta Kudu ya tabbatar cewa sun soma gudanar da bincike game da ikirarin da wasu masu gudanar da bincike a kasar Libya suka yi.

'Yan kasar Libya sun yi ammanar cewa kadarorin da aka kiyasta sun fi dala bilyan daya na marigayi Muammar Gaddafi da kuma mutanen dake da kusanci da shi ,na ajiye a kasar Afrika ta Kudu .

Wata jarida a kasar Afrika ta Kudu na Sunday Times ta ce masu binciken sun gano tsabar kudi, da gwal da kuma diamond mallakar kasar Libya a wasu bankuna hudu da kuma wasu kamfanonin zuba jari a kasar.

Jaridar ta Sunday Times ta ce masu gudanar da bincike na ganin mutumin dake kula da asusun ajiyar Gaddafi na Banki watau Bashir Al Shrkawi na rike da wani kaso na kudin.

Yana kuma cikin jerin mutanen da hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa watau Interpol take nema ruwa a jallo sai dai jaridar ta ce an sha ganinsa da manyan jami'an jam'iyyar ANC mai mulki a kasar.

Jaridar ta Sunday Times ta ce masu bincike daga kasar Libya sun gana da manyan jami'an gwamnati na kasar Afrika ta Kudu ciki har da Shugaba Jacob Zuma . Sai dai ba a samu damar jin ta bakin kakakin Shugaba Zuma game da lamarin ba.