A neman takaita cinikin makamai a duniya

Fiye da kasashe 60 ne suka sanya hannu a wata yarjejeniyar dubban biliyon daloli a kan cinikin makamai a duniya.

Wannan matakin dai, ya samu goyon bayan daga wajen kungiyoyin kare hakkin bil adama da kuma na agaji.

A watan Afrilu ne, majalisar dinkin duniya ta amince da wasu sabbin ka'idoji kan fitar da makamai zuwa kasashen waje.

Kasashe uku ne kawai basu amince da yarjejeniyaba-- wadanda suka hada da---- Iran da Syria da kuma Koriya ta Arewa.

Yayin da kashe 23 kuma suka kauracewa kada kuri'ar.