Bozize ya fice daga Kamaru

Image caption Francoiz Bozize

Hambararen Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize wanda ke zaman gudun hijira a Kamaru, ya fice daga kasar zuwa wani masaukin da ba a bayyana ba.

Shugaban ya fice ne daga Kamaru kwanakin kadan bayan sabbin hukumomin Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika su tayi shelar kamashi bisa zargin aikata laifuka a lokacin mulkinshi.

A watan maris ne hadakar kungiyoyin 'yan tawaye wato SELEKA karkashin jagorancin Michel Djotodia suka kwace mulki a hannu Bozize.

Karin bayani