Amurka ta yi shelar tukwicin dala miliyan 23

boko haram
Image caption Wasu mayakan kungiyar da ake kira Boko Haram

Gwamnatin Amurka ta yi shelar ba da tukwicin kimanin dala miliyan ashirin da uku ga duk wanda ya taimaka aka yi nasarar kame jagororin wasu kungiyoyin da ake zargi da aikata ta'addanci a kasashen Yammacin Afrika.

Tukwiuci mafi tsoka shi ne na dala miliyan bakwai da kasar ta Amurka ta ce za ta baiwa duk wanda ya taimaka wajen gano Imam Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah Lida'awati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram.

Daga cikin wadanda kasar Amurkar ta yi yayin ba da tukwicin a kansu har da tsohon dan gwagwarmayar nan mai ido daya na kungiyar Al Qaeda, Mokthar Belmokathar, wanda ake zarginsa da hannu wajen kai hari a matatar iskar gas a kasar Algeria da kuma jagoran kungiyar Al Qaeda a yankin Maghreb Yahaya Abou Al Hammam wanda ake zargin yana da hannu a kisan da aka yiwa wani dattijo bafaranshe a Jamhuriyar Nijar a shekarar 2010.

Rahotanni sun ambato wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Amurka yana cewa aikace-aikacen wadanannan 'yan gwagwarmayar sun na bakantawa Amurakar rai a don haka Amurkar zata yin duk iyakacin kokarinta na ganin ta samu bayannan da za su kaiga cafke wadannan 'yan gwagwarmayar

Gwamnatin Amurka ta kuma nuna damuwa game da yadda kungiyoyin Musulmai masu gwagwarmaya dake ci gabayaduwa a Mali da sauran wasu sassa a yankin Sahel tun bayan hambarar da gwamnati a Bamako