Gobara ta lakume kasuwar Makola a Ghana

Image caption Ana yawan samun tashin gobara a Ghana

Hukumomi a kasar Ghana sun bukaci 'yan kasuwa su kwantar da hankalinsu, yayinda suke ci gaba da binciken musabbabin wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar Makola lamba two dake birnin Accra.

A jiya (Talata) da dare ne gobarar ta tashi kuma har wayewar garin yau ta ci gaba da ci, ina ta haddasa asara mai dimbin yawa.

Barkewar gobara dai na neman zuwa ruwan dare a wasu kasuwanni na kasar ta Ghana musamman a birnin na Accra, inda cikin wata guda aka samu tashin gobara a kasuwanni har sau shidda.

'Yan kasuwa da dama sun tafka hasara sakamakon tashin gobarar.

Karin bayani