An baiwa majalisa rahoto a kan tsarin mulki

Image caption Majalisar dokokin Najeriya

A Najeriya kwamitin da majalisar dattawan kasar ta kafa don yin gyara ga kundin tsarin mulkin ya mika wa zauren majalisar rahotonsa.

Rahoton dai ya kunshi shawarwari ne ciki har da batun kirkirar sababbin jihohi da makomar wa'adin shugaban kasa.

A bara ne majalisar dattawa da ta wakilan Najeriyar suka saurari ra'ayoyin jama'a game da yin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar.

Daga cikin shawarwarin da kwamitin ya baiwa majalisar hadda baiwa kananan hukumomi damar cin gashin kai da kuma da kuma tsayar da wa'adin mulkin shugaban kasa zuwa shekara shida.

Karin bayani