An kama wasu 'yan Najeria a Amurka

A Amirka, an tuhumi tsohon babban jami'in tsaron filin jirgin saman Kotoka na Ghana da laifin fataucin miyagun kwayoyi.

Hukumomin Amirkan sun kama Solomon Adelaquaye ne, tare da wasu 'yan Najeriya biyu da kuma wani dan kasar Colombia.

A shekaru goman da suka wuce fataucin miyagun kwayoyi ya kasance wata babbar matsala a Ghana.

A cewar majalisar dinkin duniya, a kowace shekara ana fataucin hodar iblis ta cocaine a yammacin Afirka wadda kudinta ya kusan kai dala biliyan daya da rabi.

Yawancinta ana kaita ne nahiyar Turai.

Dan Ghanar da aka kama a baya bayan nan an ce Darekta ne na wani kamfani da ke tabbatar da tsaro a filin jirgin saman Kotoka na Accra.

Shugabannin filin jirgin sun katse hulda da kamfanin awoyi kamin labarin kama shi ya bazu.