Burtaniya za ta biya diyya ga 'yan Mau-Mau na Kenya

Mau mau Kenya
Image caption Wasu 'yan gwagwarmayar Mau Mau a gaban wata kotu a Landan

Gwamnatin Birtaniya za ta biya diyyar fam miliyan ashirin ga dubban 'yan kasar Kenya wadanda aka gana wa azaba aka kuma ci zarafinsu, a lokacin boren Mau-Mau, na nuna adawa da mulkin mallaka a shekarun 1950.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague, yayin da yake magana a majalisar dokoki ya ce yayi Allah-wadai da babbar murya da abin da ya kira dabbanci da fin karfi mai tayar da hankali da aka nuna a Kenya, karkashin mulkin mallakar Birtaniya.

Wani kamfanin lauyoyi na Birtaniya ne yake wakiltar 'yan Kenyan su fiye da dubu biyar, kuma kwanan nan Ma'aikatar harkokin Waje ta tabbatar da cewa ana yunkurin sasantawa.

'Yan gwagwamayar ta Mau Mau sun shigar da kara ne a gaban wata Kotu a birnin London a bara, suna zargin cewa an gana masu azaba kuma an yi musu dandaka.

A hukuncin da kotun ta yanke ta nemi a biya su diyya.