An kwantar da mijin sarauniya a asibiti

Yerima Philip
Image caption Yerima Philip

An kwantar da Yerima Philip, maigidan sarauniyar Ingila, a asibiti a nan London domin yi masa tiyata. Ana tsammanin Yeriman mai shekaru 91 a duniya zai shafe makwanni biyu a asibiti.

Wakilin BBC a fadar sarauniyar, ya ce za a yiwa Yeriman tiyata ranar juma'a ne.

A cikin wata sanarwa da ta fitar fadar Buckingham ta ce za a dunga bayar da karin bayani a lokacin da ya dace.

Dama dai ranar litinin ne, Yeriman ya janye daga wata ziyara da aka shirya zuwa cibiyar bincike ta masu fama da makanta, bayan da ya ji jikinsa ba dadi.

Wakilin BBC a fadar ya ce a lokacin da aka kai Yeriman asibiti, da kafarsa ya sauka daga mota ya taka ya shiga asibitin.