Amurka ta bukaci Iran da Hezbollah su janye daga Syria

Fadar Whte House
Image caption Jay Carney ya ce Hezbollah abokan shugaba Assad ne a kama karyar da yake yi

Amurka ta bukaci Iran da aminiyarta, kungiyar Hezbollah, su janye dakarunsu daga Syria, inda suke taimakon dakarun Shugaba Assad yakar 'yan tawaye.

Kakakin Fadar Gwamnatin Amurka ta White House, Jay Carney, ya bayyana mayakan na Hezbollah da cewa abokan Shugaba Assad ne a kama-karyar da yake yi.

Shi ma Sakatare Janar na Kungiyar Kasashen Larabawa, Nabil Al Araby, ya yi Allah-wadai da ayyukan kungiyar ta Hezbollah.

Mayakan Kungiyar Hezbollah sun taimakawa dakarun gwamnati na Syria sake karbe iko da garin Qusair mai muhimmanci dake kan iyaka da Lebanon ranar Laraba.

Image caption Taswirar dake nuna muhimmancin Qusair a Syria

Yan tawayen dai sun janye ne daga garin bayan makonni biyu da aka shafe ana ba ta kashi tsakanin bangarorin biyu duk da cewa sun shafe kusan shekara daya suna rike da garin.