Sarauniya Elizabeth ta kaddamar da hedikwatar BBC

Sarauniya a dakin watsa labarai na BBC
Image caption Sarauniya a dakin watsa labarai na BBC

Sarauniya Elizabeth ta kaddamar da sabuwar hedkwatar BBC da ke nan tsakiyar London.

A cikin jawabin da ta yi kai tsaye daga wani dakin watsa labarai ta rediyo, Sarauniyar ta ce, tana fatan BBC za ta dade tana cin amfanin sabon ginin.

Sarauniya Elizabeth din ta saurari kadaden da aka shirya mata kai tsaye, kuma ta zazzagaya ta ga dakunan watsa labarai.

Ita kadai ta yi wannan ziyarar, saboda maigidanta Yarima Philip, yana can asibiti ana yi masa tiyata.

Ana jin cewa, Yariman, wanda a ranar Litinin zai cika shekaru tasa'in da biyu a duniya, zai kwashe kimanin makonni biyu a asibitin.