Dubban 'yan Tukiyya sun tarbi Erdogan

Image caption Erdogan ya ce masu zanga-zangar sun sace kayayyakin jama'a

Dubban magoya bayan Firayim Ministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ne suka tarbe shi a filin jirgin saman Santanbul lokacin da ya koma kasar bayan ziyarar da ya kammala a arewacin Afirka.

Tarbar da magoya bayan nasa suka yi masa, ita ce wani gagarumin taro na farko da aka gudanar a kasar don goyon bayan Mista Erdogan tun lokacin da aka fara mummunar zanga-zanga a makon jiya, inda aka bukaci ya sauka daga mulki.

Magoya bayan Mista Erdogan dai sun yi tur da masu zanga-zangar, suna masu bayyana su da cewa 'yan koren makiya Turkiyya ne kuma ba za su taba samun biyan bukatunsu ba.

A wani jawabi da ya gabatar a filin jirgin saman, Mista Erdogan ya zargi masu zanga-zangar da sace kayayyakin a kantuna, da kuma yin illa ga harkokin kasuwancin kasar.

Gabanin saukar tasa dai, masu zanga-zangar sun taru a dandalin Taksim a dare na takwas, suna masu zargin Mista Erdogan da jam'iyarsa ta Justice and Development da yin mulkin kama-karya.

Karin bayani