''Amurka na tatsar bayanan jama'a ta intanet''

Image caption Jaridun sun ce jami'an leken asirin Amurka sun shafe shekaru shida suna tatsar bayanan jama'a.

Jaridar Washington Post ta Amurka da The Gurdian ta Burtaniya sun ce hukumomin leken asirin Amurka na tatsar bayanan jama'a daga manyan kamfanonin intanet guda tara, wadanda suka hada da Microsoft da Yahoo da Google da kuma Facebook da nufin bibiyar daidaikun mutane.

Jaridun sun bayar da cikakken bayani game da wani shirin gwamnatin Amurka da ake zargin na sirri ne da aka fi sani da PRISM, inda ake amfani da bidiyo da hotuna da sakon email domin bibiyar wadansu mutane.

Sun bayyana cewa jami'an leken asirin kasar sun shafe shekaru shida suna gudanar da wannan shiri, kodayake kafafen sada zumunta na Facebook da Apple sun ce ba sa bai wa hukumomin leken asirin damar shiga kai-tsaye cikin rumbunan ajiye bayanansu.

Ita dai gwamnatin Amurka, ta bakin daraktan hukumar leken asirin kasar, James Clapper, ta bayyana labarin da Washington Post ta bayar da cewa na kanzon kurege ne.

Ya kara da cewa wannan labari ka iya yin dadaddiyar illa ga jami'an tsaro da ke kokarin kawar da barazanar tsaron da ke fuskantar kasar.

An dade ana zarginsu da tatsar bayanan mutane

Wadansu jami'an gwamnatin Amurka sun shaidawa BBC cewa kodayake wata kotun kasar ta bai wa hukumomi damar samun bayanan wayar sadarwa na miliyoyin Amurkawa, amma hakan bai hada da sauraren hirarrakin da mutane ke yi ta waya ba.

Jami'an sun kara da cewa tattara irin wadannan bayanai ya taimakwa Amurka wajen kaucewa hare-haren 'yan ta'adda.

Masu rajin kare hakkin dan adam dai sun dade suna cewa jami'an tsaron Amurka na sauraren hirarrakin jama'a ta na'urorin intanet, kodayake wannan shi ne karo na farko da aka samu gamsassun shaidu da ke nuna hakan.

Karin bayani