Ana tattaunawa tsakanin gwamnati da Azbinawa

Image caption Azbinawa a lokacin tattaunawar

An soma tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Mali da Azbinawa 'yan aware dake rike da garin Kidal mai matukar muhimmanci.

Shugaban Burkina Faso, Balise Compaore dake shiga tsakani a birnin Ouagadougou yayi kiran a kawo karshen fada tsakanin bangarorin biyu domin a samu damar gudanar da zaben shugaban kasar cikin watan gobe.

An dai gwabza fada sosai cikin 'yan kwanakin nan, yayin da dakarun gwamnatin Mali suke nausawa zuwa garin Kidal.

A shekara ta 2012 ne,i Azbinawa 'yan tawaye da masu kaifin kishin Islama suka kwace iko da mafi yawancin arewacin Mali kafin dakarun Faransa su taimaka wajen fatattakarsu.

Karin bayani