Nelson Mandela ya kwana a asibiti

Image caption Mandela na cikin mummunan yanayi amma ba a tsammanin yanayin zai kara rincabewa.

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela, ya kwana a asibiti yana samun kulawar likitoci, bayan da cutar data shafi huhu da yake fama da ita, ta sake dawo masa.

Ana kallon Mandela a matsayin uban kasa wanda ya jagoranci sauyin mulki a cikin kasar daga wajen tsiraru farar fata don komawa tafarkin mulkin demokradiyya.

Wata sanarwa data fito daga fadar shugaban Afrika ta Kudu dai ta bayyana cewar likitoci na iyaka kokarinsu don ganin cewar ya samu lafiya.

Mista Mandela ya kamu da tarin fuka ne lokacin daya shafe shekaru 27 a kurkuku yana jagorantar yaki da mulkin danniya na turawan mulkin mallaka.

Wannan ne karo na uku a bana da aka kwantar da Mista Mandela a asibiti.

Karin bayani