Shugabannin Amurka da China suna taro

Image caption Shugabannin na fatan inganta dangatakar da ke tsakanin kasashen

Shugaban Amurka, Barack Obama, da takwaransa na kasar China, Xi Jinping, na gudanar da taron kwanaki biyu a jihar California.

Shugabannin za su mayar da hankali ne kan yadda za a magance matsalolin satar bayanan kwamputa da kasuwanci da Korea ta arewa da kuma tekun kudancin China.

Wannan lokaci zai kasance wata dama ga wadannan shugabanni don inganta dangantakar da ke tsakanin kasashensu.

A baya dai ana zargin China da kai hari kan kwamputocin Amurka, don haka wannan taro zai zama wata hanya ta sasantawa tsakanin kasashen da ma kaucewa faruwar hakan nan gaba.

A kwanakin baya shugaba Xi ya shaidawa wadansu manyan jami'an gwamnatin Amurka cewa akwai bukatar samun sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Ba a fiye samun damar da wadannan shugabanni za su zauna waje guda don yin tattaunawar keke-da-keke ba, don haka haduwarsu waje guda tana da matukar muhimmanci, kasancewa tattalin arzikin duniya ya dogara da yadda kasashen suke gudanar da dangantakarsu —mai kyau ko maras kyau.

Karin bayani