Anyi taro akan samar da abinci mai gina jiki

Image caption David Cameron, praministan Burtaniya

Yayin wani taron ƙasa-da-ƙasa a nan London, Birtaniya tayi alƙwarin bada kusan dala miliyan ɗari shida domin tallafawa wajen ciyar da yara ƙanana dake rayuwa cikin yanayi na fatara.

Sakatariyar gwamnatin Birtaniya mai kula da cigaban ƙasashen duniya, Justine Greening tace, rashin abinci mai gina jiki yana katsewa yara kanana damar yin rayuwa mai ingaci.

Yayin taron a nan London masu bada gudunmawa sun yi alkawarin bayar da tallafin dala biliyan hudu nan da shekara ta 2020.

Duk da irin bunƙasar tattalin arzikin wasu ƙasashen Afurka, yara ƙanana a nahiyar su kusan miliyan uku ne suke mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki a kowacce shekara.