An kashe mutane hudu a Birnin Gwari

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya rahotanni na cewa, an kashe kimanin mutane hudu yayin da wasu 'yan bindiga suka kai hari a kauyukan Goron Dutse da kuma Gwaska dake cikin karamar hukumar Brnin Gwari dake jahar Kaduna.

Rahotanni dai sun nuna cewa, mamaya 'yan bindigar suka kai, inda suka kona kusan rabin garin Goron Dutse, abinda ya tilastawa jama'ar garuruwan watsewa cikin dazuzzuka.

A yanzu dai kananan yara da mata kimanin 120 ne ke zaune a wani sansani kusa da fadar Sarkin Birnin Gwari wadanda suka gudo daga wuraren da aka kai harin.

Wani mazaunin Goron Duste ya shaidawa BBC cewar lamarin ya auke ne da subahin ranar Asabar.

Rahotanni na nuna cewar an tura jami'an tsaro garuruwan da kwantar da tarzomar.

Karin bayani