Ministan China ya gurfana a gaban kotu

Image caption Ana zargin Liu Zhijun da cin hanci da rashawa

Tsohon Ministan harkokin sufurin jiragen kasa na China, Liu Zhijun, ya gurfana a gaban kotu a Beijing, a kan tuhume tuhumen aikata rashawa da kuma yin amfani da ofishinsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Ana zargin Mista Liu da karbar na goro da kuma bai wa makusantansa kwangiloli masu tsoka.

An dai sallame shi daga aiki ne shekaru biyu da suka gabata, kuma daga bisani aka kore shi daga jam'iyyar Kwaminisanci.

A karkashin jagorancinsa ne aka yi aikin gina layukan dogo mafi tsada a China, amma suka soma fuskantar suka sosai bayan da wasu jirage biyu suka yi hatsari a watan Yulin shekarar 2011 inda mutane arba'in suka mutu.

Karin bayani