Obama ya gargadi China

Image caption Obama ya ce dole China ta kawo karshen harin da take kai wa Amurka ta intanet

Shugaban Amurka Barack Obama ya gargadi China cewa za a fuskanci gagarumar matsalar tattalin arziki idan ba ta daina satar bayanai daga cibiyoyin soji da na kasuwancinta ta hanyar intanet ba.

Mista Obama ya yi wannan gargadi ne a lokacin da suke kammala taron kwanaki biyu da takwaransa na China, Xi Jingping, a California.

Mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaron kasa, Thomas Donilon, ya ce shugaba Xi ya shaidawa Mista Obama cewa za su duba korafe-korafen Amurka game da satar bayanai ta intanet.

China ta ce ita ma tana fama da masu kai mata hare-hare ta intanet.

Wani babban jami'in gwamnatin China, Yang Jiechi, ya shaidawa manema labarai cewa bai kamata batun ya zama wani abu da zai sanya zargi da ka-ce-na-ce a tsakanin kasashen ba.

Karin bayani