Turkiyya: An yiwa masu zanga-zanga kashedi

Image caption Recep Tayyip Erdogan, Praministan Turkiyya

Praministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya yiwa masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnati kashedin cewa, zasu fuskanci hukunci saboda cigaba da zanga-zangar da suke yi.

Yayin da aka shiga rana ta goma ana tarzomar nuna adawa da gwamnati, dubban zanga-zanga suna hallara a dandalin Taksim dake birnin Santanbul.

Recep Tayyip Erdogan yayi jawabi ga dimbin magoya bayansa a birnin Ankara.

Erdogan ya bayyana masu zanga-zangar a matsayin masu daukar kayan da ba na su ba, da yace, suna neman cika kasar da tashin hankali.