Kotu a Kuwaiti ta daure wata mata kan laifin zagin Sarkin kasar

Sarkin Kuwaiti,Sheikh Sabah al-Ahmad al-Sabah
Image caption Sarkin Kuwaiti, Sheikh Sabah al-Ahmad al-Sabah

Wata kotu a kasar Kuwait ta yankewa wata mata hukuncin daurin shekaru goma sha daya a gidan yari saboda ta zagi sarkin Kuwait din a shafin sada zumunta na Twitter.

Matar mai suna Huda Al-Ajmi mai shekaru 37 da haihuwa wadda kuma malamar makaranta ce an kuma same ta da yunkurin yiwa gwamnati juyin mulki da kuma in zarafin wata darikar addini.

Tana dai da damar daukaka kara.

A yan watannin bayan nan dai Kuwait ta hukunta masu amfani da shafin Twitter da dama bisa zargin sun zagi sarkin kasar Sheikh Sabah al-Ahmad al-Sabah.