Turkiyya: 'Yan sanda a Dandalin Taksim

'Yan sanda sun kutsa kai cikin Dandalin Taksim
Image caption 'Yan sanda sun kutsa kai cikin Dandalin Taksim

’Yan sandan kwantar da tarzoma na Turkiyya sun kutsa kai cikin Dandalin Taksim da ke birnin Santanbul wanda masu zanga zanga suka mamaye sama da mako daya.

Wani wakilin BBC a Dandalin ya ce ’yan sandan na ta harba hayaki mai sa hawaye da mesar ruwa a wani yunkuri na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.

Sun kuma yayyaga kyallayen da masu zanga-zangar suka rataya, sannan suka maye gurbinsu da tutocin kasar da kuma hotunan uban kasa, Kemal Ataturk.

Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan da Firayim Ministan kasar, Recep Tayyip Erdogan, ya amince ya gana da shugabannin masu zanga-zangar adawa da gwamnati domin kawo karshen rikicin.

Karin bayani