Najeriya na fuskantar koma-baya a fannin ilimi —UNESCO

Image caption UNESCO ta ce 'yan Najeriya ne koma-baya a cikin kasashen da ke zuwa makaranta.

Hukumar raya Ilimi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta ce Najeriya ce kasar da tafi kowacce kasa a duniya adadin yaran da ba sa zuwa makaranta, ko kuma suke barin karatu.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sabon rahoto da ta fitar ranar Litinin, tana mai cewa har yanzu akwai jan-aiki wajen magance matsalar rashin shigar da yara makaranta da kuma yadda yaran kan watsar da karatu tun ba su kammala ba.

UNESCO ta kara da cewa akwai yara kimanin miliyan hamsin da bakwai da ba sa zuwa makaranta a duniya, fiye da rabinsu kuma suna nahiyar Afirka ne.

Hukumar ta ce abin da ke kara dagula lissafi shi ne yadda ake samun raguwar taimakon kudaden da manyan kasashe da kungiyoyi kan bayar wajen kyautata ilimin yara a matakin farko.

''Dalilin da ya sa na daina zuwa makaranta''

Wata yarinya 'yar shekaru 14 a duniya da wakilinmu, Is'haq Khalid, ya tuntuba ta ce ta daina zuwa makaranta ne shekaru uku da suka gabata lokacin tana aji shida na makarantar firamare.

A cewarta, '' iyayena ba su da halin biyan kudin makaranta ta shi yasa na daina zuwa.Yanzu ina zaune a gida ina taya mahaifiya ta aiki. Kuma ina zuwa tallan kayan miya''.

Ta kara da cewa tana matukar bakin ciki na rashin kammala karatunta musamman idan ta ga 'yan ajinsu da suka kammala makarantar.

Masana sun dora alhakin rashin zuwa makarantar yara kan hukumomi da iyaye, suna masu cewa hakan zai yi matukar illa ga kasar.

A cewar malam Bala Sulaiman Dalhat, na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, '' yara ne manyan gobe, kuma dole sai da ilimi ne za su zama mayan goben.Idan yara ba su samu karatu ba, nan gaba zai yi wahala a samu wadanda za su yi jagoranci na gari''.

Karin bayani