Edward Snowden ya bata sama ko kasa a Hong Kong

Edward Snowden
Image caption Tsohon jami'in CIA

Tsohon jami'in kwantaragi na hukumar leken asirin Amirka ta CIA Edward Snowden wanda ya fallasa cikkakun bayanai na shirin leken asirin Amirka ya bar Otel din da yake a Hong Kong kuma a yanzu ba a san inda yake ba.

Mista Snowden ya ce yana zaton hukumomin Amirka za su yi kokarin hukunta shi.

Hong Kong dai na da yarjejeniya da Amirka ta mika mata dukkan wanda take zargi da laifi.

Sai dai kuma lauyoyi sun ce duk wani yunkuri na tasa keyar Mr Snowden zuwa Amirka zai dauki lokaci ko ma watanni mai yiwuwa ma kuma China ta toge wajen hana aukuwar hakan.

Nicolas Bequelin na kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ya ce ya yi mamaki da Mr Snowden ya zabi zuwa Hong Kong domin mafaka.

Tun farko dai Ma'aikatar shari'a ta Amirka na bincike kan wasu bayanai da aka killace na sirri da wani jami'n leken asiri dake yiwa Amirka aikin kwantaragi ya fitar.

Jami'in Edward Snowden ya baiyanar da kansa ne bayan da a makon da ya gabata ya sanar da cewa hukumomin leken asirin Amirka na suna bin diddigi da sauraron miliyoyin wayoyin jama'a da sakonnin email da sauran hanyoyin sadarwa.

Mr Snowden ya kare kudirinsa na fitar da bayanan yana mai cewa Amirkawa na kassara ikon gwamnatoci da yin barazana ga dimokradiyya.

Ina da cikakkun bayanai game da sirrin Amurka

Sai dai a nasa martanin, Mista Snowden, ya ce ya yi hakan ne ba da nufin yin gilla ga kasar ba.

A cewarsa, ''na samu damar ganin cikakkun bayanai kan duk mutumin da ke aiki da hukumar leken asirin Amurka da hanyoyin da suke amfani da su don ganin sirrin mutane a duk duniya da kuma muradinsu. Don haka da a ce ina son yi wa Amurka illa da tuni na yi. Amma ba haka ne buri na ba.''

Mista Snowden ya bayyana matukar rashin jin dadinsa musamman ga shugaba Obama saboda rashin daukar mataki a kan batun duk da cewa ya san abubuwan da ke faruwa.

Ya yi kira ga gwamnatin Amurka ta sake tunani game da binciken da take yi a kansa.

Rahotanni na cewa a halin da ake cikin Mista Snowden na zaune a wani otal da ke Hong Kong, kuma ya ce zai nemi mafakar siyasa a duk kasar da ke bai wa mutane 'yancin fadin albarkacin bakinsu.

Karin bayani