Ana ci gaba da artabu da masu zanga-zanga a Turkiya

Masu zanga-zanga a Turkiya

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun harba konson hayaki mai sa hawaye akan gungun dubban jama'ar da ke zanga-zangar adawa da gwamnati, wadanda suka yi dandazo a dandalin Taksim a tsakiyar birnin Santanbul bayan shafe tsawon ranar yau suna artabu.

Shigar 'yan sanda dandalin ya zo ne bayan da Firaminista Recep Tayyip Erdogan ya yi kashedin cewa hakurin da yake yi da masu zanga-zangar yana neman karewa bayan da suka shafe kwanaki goma sha daya suna zaman dirshan.

Masu zanga zangar sun ci alwashin babu gudu ba ja da baya.

Wani mai zanga-zangar ya ce "Ban sa ran Firaminista Erdogan zai sauya, ba za mu sake amincewa da shi ba.

"Mun yi imani da kanmu, mun kwace wannan dandali ta hanyar gwagwarmaya, kuma daga yanzu duk matakin da 'yan sanda za su dauka za mu cigaba da gwagwarmayarmu ba za mu ja da baya ba."