Saudiyya ta rage yawan mahajjatan Najeriya

Image caption Mahajjata

Hukumar Alhazai ta Nijeriya ta tabbatar da cewa hukumomin Saudiyya sun yanke shawarar rage yawan mahajjata aikin bana da kashi ashirin cikin dari.

Sannan kuma za su rage yawan mahajjata na cikin gida da kashi hamsin cikin dari.

Hukumomin Saudiyar na cewa sun dauki matakin hakan ne a sakamakon ayyukan da suke gudanarwa na fadada masallacin Haram da ma sauran wuraren ziyarar ibada.

Alhaji Abdullahi Mukhtar Muhammad, kwamishinan gudanarwa na hukumar Alhazan Nijeriya, ya ce a maimakon mutane dubu casa'in da biyar da ake sa ran za su je aikin hajjin bana daga Nijeriya, mutane dubu saba'in da shidda ne za a dauka.

Karin bayani