Mandela na murmurewa! Inji Zuma

Nelson Mandela
Image caption Tsohon shugaban kasar Afurka ta Kudu

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma yace Nelson Mandela na samun sauki dangane da maganin da ake masa na ciwon huhu.

Mr Zuma ya shaidawa majalisar dokoki cewa ya yi farin ciki da cigaban da Mandelan ke samu bayan abin da ya kira yan kwanaki masu tsanani da Mandelan mai shekaru 94 a duniya ya shiga.

Iyalan dattijon wanda ake kallonsa da kima da martaba sun ce sakonnin fatan alheri da suka rika samu daga sassan duniya sun kara musu karsashi da kwarin gwiwa. Mandla wanda jika ne ga Mandela ya yi godiya ga wadanda ke kula da kakan nasa

Karin bayani