Abubuwa sun kyautatu a birnin Yamai

Image caption Jami'an tsaro a Nijer

A Jamhuriyar Nijer, abubuwan sun daidaita a rundunar horadda jandarmomi dake unguwar Kwara Tagi dake birnin Yamai, bayan wasu 'yan bindiga sun kai hare a wajen.

A daren ranar Talata ne, aka yi musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da wasu 'yan bindiga a harabar rundunar horadda jandarmerin.

A yanzu dai, zirga-zirga ta komo a unguwar, sai dai kawo yanzu hukumomi Nijer din, basu yi karin bayani game da lamarin ba.

A 'yan watannin nan, an soma samun tabarbarewar tsaro a Nijer, inda aka kai hari a gidan kaso na Yamai, da wajen hako ma'adinai na Arlit.

Karin bayani