Za mu share Dandalin Taksim —Gwamnan Santanbul

'Yan sandan Turkiyya na harba barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zanga
Image caption 'Yan sandan Turkiyya sun yi ta harba barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zanga

’Yan sanadan kwantar da tarzoma a Turkiyya sun ci gaba da arangama da masu zanga-zanga har cikin daren ranar Talata a Santanbul—inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da mesar ruwa don kawar da dubban mutanen da suka taru a Dandalin Taksim.

Da dama daga cikin masu zanga-zangar dai sun koma Dandalin Shakatawa na Gezi da ke makwabtaka da Dandalin na Taksim.

Yayinda ’yan sandan ke amfani da hayaki mai sa hawaye da mesar ruwa, wadansu daga cikin masu zanga-zangar kuwa jifan ’yan sandan da duwatsu da kuma bama-baman kwalba suka yi ta yi.

Wannan taho-mu-gama kuma ta rutsa da dubban masu zanga-zangar lumana, da ma’aikatan sa-kai wadanda suka kakkafa asibitoci na wucin-gadi don kula da wadanda suka jikkata.

Da yake magana a gidan talabijin na kasa, Gwamnan Santanbul, Huseyin Avni Mutlu, ya ce ’yan sandan za su ci gaba da aikin da suke yi har sai an share Dandalin Taksim.

“Ina kira ga jama’a da su kaurace wa Dandalin Taksim har sai an maido da cikakken tsaro.

“Za mu ci gaba da daukar mataki dare da rana har sai an kawar da kungiyoyin ’yan tsiraru, kuma ina kira ga jama’a su taimaka wa ’yan sanda yayin da muke daukar wannan mataki”, inji Mista Mutlu.

Firayim Minista Recep Tayyip Erdogan, wanda ke fuskantar kalubale mafi tsanani a mulkinsa na fiye da shekaru goma a kasar, ya ce wajibi ne a kawo karshen zanga-zangar ba tare da bata lokaci ba. Sai dai babu alamar faruwar hakan.

Kwanaki goma sha biyu da suka wuce ne dai aka fara zanga-zangar a Dandalin Shakatawa na Gezi, don nuna rashin amincewa da shirin gwamnati na sake fasalin dandalin.

Amma daga bisani ta yadu, inda masu zanga-zangar suka zargi Mista Erdogan da yunkurin kakaba akidunsa na Musulunci a kan kasar mai bin akidar raba siyasa da addini.

Karin bayani