Nilu: Taƙaddama tsakanin Masar da Habasha

Image caption Kogin Nilu

Majalisar dokokin Ethiopia ta kawar da wata yarjejeniya da aka ƙulla tun zamanin mulkin mallaka wacce ta baiwa Masar da Sudan iko da mafi yawan kogin Nilu.

'Yan siyasar kasar Masar dai sun nuna damuwa sosai dangane da shirin Ethiopia na gina sabuwar madatsar ruwa a kogin na Nilu, suna cewa, yin hakan tamkar ƙaddamar da yaki ne akan kasar Masar.

Gwamnatin Masar tayi gargadin cewar aikin zai rage samun ruwan Masar, kuma wasu yan siyasa sun bayar da shawarar lalata madatsar ruwan.

Ministan harkokin wajen Masar zai tafi Addis Ababa domin tattaunawa ranar lahadi.